An Kawo Karshen Kuri'ar Raba Gardama A Yankin Darfur Na Kasar Sudan
(last modified Thu, 14 Apr 2016 05:02:57 GMT )
Apr 14, 2016 05:02 UTC
  • An Kawo Karshen Kuri'ar Raba Gardama A Yankin Darfur Na Kasar Sudan

Rahotanni daga kasar Sudan sun bayyana cewar an kawo karshen kuri'ar raba gardama da gwamnatin kasar ta gudanar kan makomar yankin Darfur, duk kuwa da kauracewa zaben da kungiyoyin 'yan tawaye suka yi suna zargin cewa gwamnatin za ta tafka magudi yayin zaben.

Gwamnatin Sudan din ta gudanar da wannan zaben jin ra'ayin al'umma din ne don abin da ta kira ba da dama ga 'yan yankin zaban ko dai a ci gaba da gudanar da mulkin yankin kamar yadda yake a yanzu inda aka raba shi karkashin jihohi biyar ko kuma a hada su a matsayin yanki guda.

Gwamnatin dai ta ce jama'a sun fito da yawan gaske yayin kada kuri'ar, inda ake sa ran a mako mai zuwa ne za a sanar da sakamakon zaben.

Matsayar da gwamnatin ta Sudan ta dauka a shekarar 1994 na raba yankin Darfur din zuwa jihohi uku ne ya haifar da rikici da yakin basasa a yankin inda wasu daga cikin al'ummomin yankin suka dau makami da kaddamar da tawaye suna zargin gwamnatin kasar da nuna musu bambanci da wariya.

Bisa kididdigan Majalisar Dinkin Duniya, sama da mutane 300,000 ne suka rasa rayukansu kana wasu miliyoyi kuma suna cikin matsanancin hali sakamakon wannan rikicin da ake zargin jami'an gwamnatin kasar ta Sudan ciki kuwa har da shugaban kasar Umar Hasan al-Bashir da aikata laifin yaki da take hakkokin bil'adama da ya sanya ake nemansu ruwa a jallo don hukunta su.