An rusa maboyar 'yan ta'adda biyar a kasar Aljeria
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3877-an_rusa_maboyar_'yan_ta'adda_biyar_a_kasar_aljeria
Dakarun tsaron Aljeria sun samu nasarar rusa sansanin 'yan ta'adda 5 a yakuna daban-daban na kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:08+00:00 )
Apr 14, 2016 09:34 UTC
  • An rusa maboyar 'yan ta'adda biyar a kasar Aljeria

Dakarun tsaron Aljeria sun samu nasarar rusa sansanin 'yan ta'adda 5 a yakuna daban-daban na kasar

Cikin wata sanarwa da ta fitar Yau, Ma'aikatar tsaro Aljeria ta ce a ci gaba da yaki da ta'addanci, Dakarun tsaron kasar sun samu nasarar rusa sansanin 'yan ta'adda biyar a yankunan Tizy, Auzu, Tibaze da haijal.

Har ila yau Dakarun tsaron sun kame na'urori leken asiri , kayan aikin soja da ababen fashewa da dama a sansanin 'yan ta'addar.

A cikin 'yan watanin nan Dakarun tsaron na Aljeria na iya kokari wajen rusa kungiyoyin 'yan ta'addada suke kokarin samun matsuguni a cikin kasar tare kuma da bada himma wajen sa'ido sosai kan iyakar kasar da kasashen Tunsiya da Libiya domin hana kwararar 'yan ta'adda shiga cikin kasar.