Jamus Zata Karfafa Ayyukan Tawagar Sojojin Ta A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3910-jamus_zata_karfafa_ayyukan_tawagar_sojojin_ta_a_mali
kasar Jamus ta ce zata kara karfafa ayyukan tawagar sojojin ta a Mali, duk da cewa zata rage yawan sojojin daga 350 zuwa 300.
(last modified 2018-08-22T06:58:08+00:00 )
Apr 15, 2016 06:33 UTC
  • Jamus Zata Karfafa Ayyukan Tawagar Sojojin Ta A Mali

kasar Jamus ta ce zata kara karfafa ayyukan tawagar sojojin ta a Mali, duk da cewa zata rage yawan sojojin daga 350 zuwa 300.

Gwanatin jamus ta ce ta damu matuka da yanayin da ake ciki a Mali, wanda ya sanya zata tura sojojin na ta dake Bamako babban birnin kasar ta Mali zuwa yankuna dake fuskantar barazana, musamen a arewacin kasar.

kazalika Jamus ta ce zata tsawaita aiki tawagar sojojin ta data kunshi masu bada horo da dakaru na musamen mai suna Bundeswehr a kasar ta Mali, koda batun na bukatar amuncewa majalisar dokokin kasar ta Jamus da zata duba shi nan gaban.