An kame dariruwan Mutane a kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3940-an_kame_dariruwan_mutane_a_kasar_mali
Dariruwan Mutane ne aka kame kan zarkin su da hannu a harin ta'addancin da aka kai Hotel Radissoun Blu dake birnin Bamako na kasar Mali
(last modified 2018-08-22T06:58:08+00:00 )
Apr 16, 2016 00:27 UTC
  • An kame dariruwan Mutane a kasar Mali

Dariruwan Mutane ne aka kame kan zarkin su da hannu a harin ta'addancin da aka kai Hotel Radissoun Blu dake birnin Bamako na kasar Mali

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto Salif traore Ministan tsaron cikin gidan Mali na cewa tun bayan kafa dokar ta bace a kasar, an kame mutane sama da dubu biyu kan zarkin su da hannu wajen kitsa harin ta'addancin da aka kai Hotel Radisson Blue dake birnin Bamako a watan Nuwambar da ya gabata, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 22.

Ministan ya ce a halin da ake ciki ana gudanar da bincike kan mutane 700, bayan da aka kama makamai kimanin 50.

Mista Traore ya ce jami'an 'yan sanda na kame mutanan da suke zarki ne su bincike su kuma tsare su na tsayon sa'o'i 48 ko 72 bayan haka su meka su a gaban kuliya domin su tunkari shara'a kan zarkin da ake yi musu.

Majalisar dokokin kasar ta Mali ta tsawaita dokar ta bacen da aka sanya bayan harin ta'addancin da aka kai Hotel Radisson din a shekaran jiya Alkhamis, bayan kai wannan hari dai kungiyar Alka'ida ta dauki alhakin kai harin.