Sojojin Nijeriya Sun Sami Gagarumar Nasara A Kan 'Yan Boko Haram
-
Nigeria Army clears Boko Haram\\\'s camp
A ci gaba da kokarin da sojojin Nijeriya suke yi na kawo karshen kungiyar nan ta Boko Haram, sojojin sun sanar da wata gagarumar nasarar da suka samu a kan 'yan kungiyar biyo bayan wani hari da suka kai daya daga cikin maboyan 'yan kungiyar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar sojan Nijeriyan Kanar Sani Usman Kukashekaya fitar, ya ce sojojin na rundunar Lafiya Dole tare da hadin gwiwan dakarun sa kai na Civilin JTF ne suka kai wannan harin a yankin Borgozo-Alargano a ranar Lahadi da ta gabata bayan wani bayanai na sirri da suka samu inda ya ce sojojin sun sami nasarar kwato wani adadi mai yawan gaske na makamai da 'yan Boko Haram din suka boye a wajen.
Kanar Kukasheka ya kara da cewa har ila yau sojojin sun sami nasarar kwato wasu kayayyakin da suka hada da motar Toyota, Janareta da wasu babura; kamar yadda kuma sun sami nasarar hallaka wasu 'yan ta'addan Boko Haram din.
Sanarwar sojojin ta bukaci al’umma da su ci gaba da taimaka musu da bayanai masu amfani domin da za su ba su damar cimma burinsu na kawar da sauran gyauron 'yan kungiyar da suka rage.
A wata sabuwa kuma babban hafsan hafsoshin sojin kasa na Nijeriyan, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, ya jagoranci bikin bude hanyar Biu zuwa Damaturu wadda ta kasance a karkashin ikon 'yan Boko Haram din tsawon shekaru ukun da suka gabata, lamarin da ake ganinsa a matsayin ci gaba da nasarar da sojojin suke samu a kan 'yan kungiyar ta Boko Haram.