Zanga-zangar nuna adawa da zaman Dakarun tsaron waje a kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4051-zanga_zangar_nuna_adawa_da_zaman_dakarun_tsaron_waje_a_kasar_mali
Al'ummar arewacin kasar Mali sun gudanar da zanga-zanga domin nuna adawarsu da ci gaban Sojojin kasar waje a cikin Kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:09+00:00 )
Apr 18, 2016 12:10 UTC
  • Zanga-zangar nuna adawa da zaman Dakarun tsaron waje a kasar Mali

Al'ummar arewacin kasar Mali sun gudanar da zanga-zanga domin nuna adawarsu da ci gaban Sojojin kasar waje a cikin Kasar

Jaridar Le figaro ta kasar Faransa ta nakalto wata majiyar tsaron Dakarun Sulhu na MDD dake Kasar ta Mali wato Munusma na cewa a wannan Litinin Al'ummar garin Kidal dake arewa maso gabashin kasar sun gudanar da zanga-zanga, inda har wani farar hula ya rasa ransa.

Ita na dai wannan zanga-zangar an gudanar da ita ne domin nuna adawa kan ci gaba da zaman dakarun kasashen waje musaman ma kasar Faransa a cikin kasar.

A bangare guda Kungiyar Munusma ta rage dakarun ta dake filin sauka da tashin na jiragen saman birnin Kidal tare da gudanar da bincike da nufin samun labarun karshen dangane da Wadanda wannan rikici ya ritsa da su.

Wannan zanga-zanga dai na zuwa a daidai lokacin da kasar ta Mali ke cikin yanayin dokar ta bace sakamakon harin ta'addancin da aka kai a watan Nuwambar shekarar da ta gabata.

Tun a shekarar 2013 ne, Dakarun tsaron kasar Faransa tare da kimanin Dakarun sulhu dubu 10 na MDD ke kasar ta Mali, amma har yanzu sun kasa tabbatar da tsaro a cikin kasar.