Mali : Anyi Zanga-zangar Kyammar Sojojin Ketare
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4081-mali_anyi_zanga_zangar_kyammar_sojojin_ketare
A kasar Mali mutun guda ne aka rawaito cewa ya rasa ran sa a yayin wata zanga-zanga kyammar sojojin kasashen waje a Kidal dake arewacin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:09+00:00 )
Apr 19, 2016 05:29 UTC
  • Mali : Anyi Zanga-zangar Kyammar Sojojin Ketare

A kasar Mali mutun guda ne aka rawaito cewa ya rasa ran sa a yayin wata zanga-zanga kyammar sojojin kasashen waje a Kidal dake arewacin kasar.

Mazauna yankin dai na adawa da ci gaba da kasancewar sojojin Faransa da na MDD dake aikin tabbatar da tsaro da yaki da ta'adanci a yankin Sahel.

Wani mazaunin Kidal ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa sojojin na MInusma suka bude kan masu zanga-zanga lamarin da yayi sanadin mutuwar akallah mutun guda.

Saidai tawagar ta Munusma wace ta tabbatar da zanga-zanga a cikin wata sanarwa ta ce tana ci gaba da bincike akan lamarin.