Wasu 'yan agajin guda uku sun batan laya a kasar Mali
Wasu Ma'aikatan kungiyar Agajin gaggawa na Kasa da Kasa guda Uku sun batan laya a kasar Mali.
Jaridar Le Figaro ta kasar Faransa ta nakalto Valery Mbaoh Nana daya daga cikin masu magana da yawun kungiyar kai agajin na cewa tun a ranar Assabar din da ta gabata ce manbobin nasu uku suka bace a yankunan dake arewacin na Mali kuma har yanzu babu wani labari a kan inda suke ko kuma su waye suka yi garkuwa da su.
Rahoton ya ce karshen ganin da ake yi manbobin na ta guda uku, a kauyen Abeibara dake kusa da garin Kidal, bayan haka har yanzu babu wani labarinsu, kafin hakan, a shekarar 2015 din da ta gabata daya daga cikin manbobin kungiyar kai agajin gaggawar ya rasa ransa a hanun kungiyar 'yan ta'adda.
A shekarar 2014 wata tawagar kungiyar Agajin gaggauwar mai gumshe da Mutane biyar an yi awan gaba da ita a arewacin na Mali, saidai bayan wattani biyu aka sallamo su.
Tun a daga shekarar 2012 ne yankunar arewacin Malin ke fuskantar matsalar tsaro biyo bayan juyin milki da aka yiwa kasar tare kuma kutsan kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin.