Shugaba Derby Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Chadi Da Aka Gudanar
(last modified Fri, 22 Apr 2016 12:18:24 GMT )
Apr 22, 2016 12:18 UTC
  • Shugaba Derby Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Chadi Da Aka Gudanar

Shugaba Idriss Derby ya lashe zaben shugabancin kasar Chadi da aka gudanar a ranar 10 ga watan Afrilun da ya gabata da gagarumin rinjaye bayan da aka sanar ya samu sama da kashi 61 cikin dari na na kuri’un da aka kada.

Rahotanni daga kasar Chadin sun jiyo majiyoyin hukumomin zaben kasar suna cewa shugaba Derby ya samu sama kashi 61 cikin dari na kuriu'n da aka kada sannan tsohon mai adawa da shugaba Saleh Kebzabo ya zo na biyu da kusan kashi 12 cikin dari yayin da magajin garin Moundou da ke kudancin kasar Laoukein Kourayo Medard ya samu kashi 10 cikin dari a zaben.

Hukumomin Zaben dai sun bayyana cewa an samu fitowar kashi 71 na wadanda suka cancanci jefa kuri’unsu a yayin wannan zaben da aka gudanar da shi.

Tun da fari ma dai an yi hasashen cewa shugaba Idris Derby, wanda tuna shekarar 1990 ya ke shugabancin kasar, ne zai lashe shi.