Bukatar Shugaban Afirka ta Kudu ga Jam'iya mai milki
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4264-bukatar_shugaban_afirka_ta_kudu_ga_jam'iya_mai_milki
Shugaban Kasar Afirka ta Kudu ya bukaci 'ya'yan Jam'iyar ANC mai milki da su magance sababin da ke tsakaninsu.
(last modified 2018-08-22T11:28:10+00:00 )
Apr 24, 2016 03:42 UTC
  • Bukatar Shugaban Afirka ta Kudu ga Jam'iya mai milki

Shugaban Kasar Afirka ta Kudu ya bukaci 'ya'yan Jam'iyar ANC mai milki da su magance sababin da ke tsakaninsu.

A yayin da zaben kananen hukumomi ke kuratowa a kasar Afirka ta kudu, Shugaban Kasar Jacob Zuma ya bukaci 'ya'yan Jam'iyarsa na ANC da su magance sabanin dake tsakaninsu, su kuma dakile duk wata baraka ta kunno kai a Jam'iyar.

Shugaba Zuma ya bukaci dukkanin 'ya'yan Jam'iyar da su yi isa kokarinsu domin ganin Jam'iyar ta samu nasara a zaben Kananan hukumomi mai zuwa.

Shugaba Jacob Zuma nada cikekken goyon bayan Jam'iyar ta sa ta ANC, lamarin da ya sanya ya tsallaka rijiya da baibai a yayin da 'yan adawa suka yi yunkurin tsige sa,inda suka kasa samun isasun kuri'un da zai sanya su tunbuke shi a kan kujerarsa.

A kwanakin baya ne dai 'yan Majalisar dokoki na bangare Adawa suka Ajiye takardar neman tsige Shugaba Zuma a kasar Afirka ta kudun,saboda samun sa da aka yi da laifin amfani da kudaden Gwamnati wajen gyaren gidansa,da hakan ya sanya kotun kundin tsarin milkin kasar ta sanar da cewa abin da Shugaba Zuman ya yi ya sabawa kundin tsarin milkin kasar.