Shugaban Kasar Alfirka ta kudu ya ce ba zai murabus ba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4468-shugaban_kasar_alfirka_ta_kudu_ya_ce_ba_zai_murabus_ba
Shugaban kasar Afirka ta Kudu ya yi watsi da bukatun 'yan adawa na sauka daga kan karagar milki.
(last modified 2018-08-22T11:28:11+00:00 )
Apr 28, 2016 03:35 UTC
  • Shugaban Kasar Alfirka ta kudu ya ce ba zai murabus ba

Shugaban kasar Afirka ta Kudu ya yi watsi da bukatun 'yan adawa na sauka daga kan karagar milki.

Kamfanin dillancin Labaran France Press daga birnin Johannesburg ya nakalto Jacib Zuma Shugaban Kasar Afirka ta kudu jiya Laraba gaban dubban magoya bayan sa na cewa domin kaucewa tayar da tashin hanhali a kasar wajibi ne a yi tunanin ci gaba da kuma kasar.

A ranar Lahadin da ta gabata, yayin da yake tattauna da 'yan jaridu, mista Julius Malama Shugaban kungiyar yaki da 'yanci tattalin arzikin kasar wato EFF bisa goyon bayan 'yan adawar Zuma ya ce za su yi amfani da makamai wajen kifar da Gwamnatin Jacob Zuwa.

Malama ya tabbatar da cewa 'yan adawa ba sa tsoron yaki kuma kuma Sojojin kasar, domin haka za su dauki niyar kifar da Shugaba Zuma ta ko wani hali.

Masu adawa da Shugaba Zuma sun kasa samun isassun kuru'u da zai sanya a tsike Shugaban Zuma a zauren Majalisar dokokin kasar wanda hakan ya sanya suka fara tunani tsike ke da karfi.

'Yan adawar na zarki shugaba Zuma da bata dukiyar kasa tare da milkin kama karya, inda suka ce za su sake gabatar da tuhumar kan bata dukiya kasa, hakan na zuwa bayan da Kwamitin bincike na yin almundana da dukiyar Kasa yayi na shekarar 2014, inda ya zarki Shugaba Zuma da bata milyoyin dala na Bajat din kasar.