Hallakar 'yan ta'addar uku a kasar Aljeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4570-hallakar_'yan_ta'addar_uku_a_kasar_aljeriya
Ma'aikatar tsaron Aljeriya ta sanar da hallaka 'yan ta'adda uku a yankin Eskida dake yammacin Alge babban birnin Kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:12+00:00 )
Apr 30, 2016 11:13 UTC
  • Hallakar 'yan ta'addar uku a kasar Aljeriya

Ma'aikatar tsaron Aljeriya ta sanar da hallaka 'yan ta'adda uku a yankin Eskida dake yammacin Alge babban birnin Kasar

A Sanarwar da ta fitar Yau Assabar, Ma'aikatar tsaron ta ce farmakin da Sojojin kasar suka kai sun samu nasarar gano wasu bindigogi kirar Kilashcop da dama tare da ababen fashewa.

A ranar Alkhamis din da ta gabata ma Ma'aikatar tsaron kasar ta sanar da hallaka 'yan ta'adda biyu da kauyan Auladu Isa dake Jihar Bumar das.

Har ila yau Sojojin na Aljeriya sun samu nasarar cabke Mutane 34 da ake zarkinsu da 'yan ta'adda ko kuma masu taimakawa 'yan ta'addar a jihar Alwadi dake da nisan kilomita 650 daga kudu masu gabashin babban birinin kasar da kuma jihar Tiziwazur mai nisan kilomita 100 daga gabashin Alge babban birnin Kasar

A baya bayan nan dai Dakarun tsaron na Aljeria sun tsanaita kai hare-hare kan 'yan ta'adda inda alkaluma ke bayyana cewa a cikin wata guda da suka gabata sun hallaka 'yan ta'adda kimanin 20 tare kuma da kama makamai da ababen fashewa masu yawan gaske.

Domin hana safarar makamai da kuma 'yan ta'adda cikin kasar,Gwamnatin Aljerian ta jibke dubun Sojojin a kan iyakokin kasar.