Harin 'Yan Sandar Masar kan 'Yan Jaridu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4642-harin_'yan_sandar_masar_kan_'yan_jaridu
Jami'an 'yan sandar Masar Sun kai harin kan ofishin kungiyar 'yan Jaridu ta kasa tare da Kame biyu daga cikin su
(last modified 2018-08-22T06:58:12+00:00 )
May 02, 2016 02:27 UTC
  • Harin 'Yan Sandar Masar kan 'Yan Jaridu

Jami'an 'yan sandar Masar Sun kai harin kan ofishin kungiyar 'yan Jaridu ta kasa tare da Kame biyu daga cikin su

Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa daga birnin Alkahira ya nakaloto Yahaya Kalash Shugaban kungiyar 'Yan Jaridun kasar Masar na cewa A jiya Lahadi Jami'an 'Yan sanda sun kai farmaki kan ofishin kungiyar 'yan Jaridu ta kasa dake birnin Alkahira, inda suka yi awan gaba da Amru badar da kuma Mahmud Assaka.

Wani Jami'in Alkalan kasar ya sanar da cewa Kotu ce ta bada umarnin kame wadannan 'yan jaridu guda biyu domin ana zarkinsu da tunzura Al'umma su gudanar da zanga-zangar nuna adawa da Gwamnati wanda kuma hakan ya sabawa dokar kasar.

Rahoton ya ce wadannan 'yan Jaridu biyu da ake kame na daga cikin 'yan Jaridun dake nuna adawa kai tsaye kan kudirin da Gwamnatin kasar ta dauka na Baiwa Saudiya Tsibiran Tiran da Sanafir.