Kin Amincewa Da Sakamakon Zaben Shugaban Kasa
May 02, 2016 18:56 UTC
Jam'iyyar hamayya ta Forum For Democratic Change a kasar Uganda ta sake jaddada kin amincewa da sakamakon zaben kasar.
Jaridar Monitor wacce ake bugawa a birnin Kamfala ta buga jawabin shugaban jam'iyyar Samojo Nganda yana cewa; Zaben shugaban kasar da aka gudanar ba halartacce ba ne.
Bugu da kari, jam'iyyar ta sake yin kira da a maimaita kidayar kuri'un da al'ummar kasar su ka kada a lokacin zaben.
A yayin zaben shugaban kasar da aka yi a watan Febrairu an sami rashin jituwa a tsakanin 'yan hamayya da kuma shugaba Yowure Museveni wanda aka sake bayyanawa a matsayin wanda ya lashe zaben.
Tags