Shugaba Zuma Ya gargadi Masu Hamayya Da gwamnatinsa
Shugaba Zuma Ya gargadi Masu Hamayya Da gwamnatinsa
kamfanin dillancin labarun Faransa ya nakalto shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma yana gargadin yan hamayya akan duk wani yunkuri ta haddasa rikici da tashin hankali.
Zuma wanda ya ke magana da dubban mutane a birnin Pretoria ya kuma ce; matukar 'yan hamayyar siyasar su ka haddasa wani rikici to gwamnati za ta yi amfani da dukkanin karfin da ta ke da shi domin fuskantarsu.
Shugaban na Afirka ta kudu dai yana maida martani akan kiran da 'yan hamayya su ka yi na a tsige shi a majalisar kasar.
A cikin watannin bayan nan dai shugaban na kasar Afirka ta kudu yana fuskanta suka daga 'yan hamayya saboda tuhumarsa da ake yi da cin hanci da rashawa.