Mali : Masu Rikici A Kidal Sun Cimma Yerjejeniyar Zaman Tare
-
\\\'yan tawayen buzaye a Mali
Bangarorin biyu dai sun sha alwashin cewa daga yanzu zasu bi ta hanyar tattaunawa domin warware duk wani sabani dake tsakanin su
Tsafin 'yan tawayen buzaye a arewacin Mali da gamayar kungiyar mayakan dake goyan bayan gwamnatin kasar sun cimma yejejeniyar zamen tare a yankin Kidal.
A wata sanarwar hadin gwiwa ta bangarorin biyu da kanfanin dilancin labaren AFp ya samu irin ta, an ce mayakan dake goyan bayan gwamnatin sun samu shiga yankin na Kidal ba tare da fuskantar wata barazana ba.
Bangarorin biyu dai sun sha alwashin cewa daga yanzu zasu bi ta hanyar tattaunawa domin warware duk wani sabani dake tsakanin su a sanarwar da jagororin su da suka da Hanoune Ould Ali da Alghabass Ag Intalla suka sama hannu.
wannan dai wani bangare ne na yerjejeniyar da aka cimma a watan Mayu bara tsakanin gwamnati da 'yan tawayen Mali.