Kasashen Larabawa Sun Bukaci Taimakon Turai Wajen Warware Rikicin Siyasar Kasashensu
Kungiyar Kasashen Larabawa ta Bukaci Majalisar kasashen Turai da ta Taimaka wajen warware rikicin dake addabar kasashen Larabawa ta hanyar Siyasa.
A yayin ganawarsa da tawagar Majalisar kasashen Turai jiya a birnin Alkahira, Mataimakin babban saktaren kungiyar kasashen Larabawa Ahmad bn Hilly ya bayyana cewa warware matsalan yankin Palastinu shine mabudin tabbatar da tsaro a yankin baki daya, wajibi ne a gudanar da bincike kan gine-gine da kuma rusa gidajen Palastinawa da mahukuntan Haramcecciyar kasar Isra'ila ke yi a yankunan Palastinawa.
Bn Hilly ya bukaci Majalisar kasashen Turan da ta yi kokari wajen samar da mafutar da ta dace a siyasance domin kawo karshen matsalar da kasashen Larabawa ke fuskanta.
Har ila yau bn Hilly ya bukaci kasashen Taurai tare da kungiyoyin kasa da kasa sun taimaka wajen magance rikicin kasashen Siriya, Yamen, Libiya da kuma Iraki ta hanyar siyasa.