Rikicin Kabilanci Yana Ci Gaba Da Lashe Rayukan Mutane A Kasar Mali
Wasu gungun jama'a da suke goyon bayan gwamnatin Mali suna ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan 'yan kabilar Peuhl da ake zargi da goyon bayan kungiyoyi masu tsaurin ra'ayin addinin Islama a kasar.
Babban sakataren wata kungiyar 'yan daba da ake kira da Dental Wuwarbe mai suna Sekou Bah ya sanar da cewa; A kwanaki biyar da suka gabata wato ranar 30 ga watan Aprilun da ya gabata an kai hari kan wasu 'yan kabilar ta Peuhl a wani wajen cin abinci, inda aka kashe hudu daga cikinsu, sannan a washe garin kisan gillar aka harbe wasu karin 'yan kabilar ta Peuhl guda tara har lahira a lokacin da suke bisine 'yan uwansu a makabarta.
Wasu rahotonni sun bayyana cewa; Wasu gungun 'yan daba da hadin bakin sojojin gwamnatin Mali sun kai hari kan 'yan kabilar ta Peuhl a yankin Mopti, inda suka kashe tare da jikkata mutane akalla tara.
A halin yanzu haka dai wasu rahotonni suna cewa; hare-haren wuce gona da iri kan 'yan kabilar ta Peuhl sun lashe rayukan mutane akalla 30 lamarin da mahukuntan kasar suka jaddada matakin gudanar da bincike kan lamarin.
Ana zargin 'yan kabilar ta Peuhl ne da goyon bayan 'yan tawayen kungiyar Macina Liberation Front masu dauke da tsaurin ra'ayin addinin Islama a kasar.