An gano makamai A Kasar Aljeriya
May 08, 2016 03:16 UTC
Sojojin kasar Aljeriya Sun Sanar da Gano Makamai A kusa da iyakar kasar Tunisiya.
Majiyar sojan kasar Aljeriya ta sanar da gano mabuyar makamai a kusa da iyakarta da kasar Tunisiya.
A wata sanarwa da ma'aikatar tsaron kasar ta Aljeriya yi a jiya asabar ta ce an gano mabuyar makaman ne a yankin al-ud da ke kan iyaka da Tunisiya. Makan dai sun kai bindigogi 131 sai kuma makamai masu linzami da albarusai.
A cikin watannin bayan dai sojojin kasar ta Aljeriya sun rika sanar da gano makamai ko kuma kashe 'yan ta'adda a sassan daban-daban na kasar.
Tags