Masar : Gobara Ta Kashe Mutane 2, Wasu 88 Sun Raunana
-
gobara a wata masana'anta a Masar
Rahotanni daga kasar Masar na cewa mutane biyu ne suka rasa rayukan, kana wasu 88 na daban suka raunana a wata mumunan gobara da ta abkama wasu mayan gine-gine biyar a tsakiyar birnin Alkahira.
tun da farko dai ma'aikatar agaji ta kasa ta ce mutane 55 ne suka raunana a gobara data tashi yau Litinin a unguwar ta yan kasuwa, saidai a cewar ma'aikatar lafiya ta kasar adadin mutanen da suka jikatta ya kai 88, kana an samu wasu gawawakin wasu mutane 2 da suka kone kurmus a cikin baraguzan ginin.
har kawo yanzu dai ba'a kai tantance musababin tashin gobara ba, data tashi a cikin daren jiya wayewar wannan safiyar a wani karamin otel dake unguwar Al'Mosky kusa da masalacin Al'Azhar.
bayanai dai sun cewa gobara da yadu da sauri ne a sauran benayen saboda kayan ajiyar dake a ciki mafi yawancin su na roba ne.
Kawo yanzu dai an kai ga shawo kan gobara bayan shafe sama da sa'o'i 12 ana kokarin kashe ta kamar yadda babban jami'an 'yan kwana kwanan na birnin Alkahira janar Gamal Halawa ya sanar tare da cewa an samu 'yan kwana-kwanan da jami'an yan sanda 16 da suka raunana.