Yan Tawayen Uganda Sun Kashe Mutane Masu Yawa A Kasar DR Congo
(last modified Tue, 10 May 2016 11:06:53 GMT )
May 10, 2016 11:06 UTC
  • Yan Tawayen Uganda Sun Kashe Mutane Masu Yawa A Kasar DR Congo

Wata cibiyar kare hakkin bil-Adama da tsarin dimokaradiyya a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta sanar da cewa: 'Yan tawayen Uganda sun kashe mutane da dama a hare haren wuce gona da irin da suka kai kan yankunan da suke gabashin kasar ta Dimokaradiyyar Congo.

Babban jami'in shiga tsakani a cibiyar kula da kare hakkin bil-Adama da sanya ido kan tafiyar tsarin dimokaradiyya a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta "CEPADHO" Omar Kavota ya sanar da cewa: A cikin makonni biyu da suka gabata 'yan tawayen Uganda da suke da sansanoni a yankunan gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun kai farmaki kan al'ummar kauyen garin Beni a da ke lardin Kivu ta arewa a gabashin kasar, inda suka kashe fararen hula da yawansu ya haura mutane 50.

Omar Kavota ya kara da cewa: Gungun 'yan tawayen kasar ta Uganda da suke da matsuguni a cikin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun kaddamar da hare-haren wuce gona da irin ne da kananan makamai, inda sai bayan wani lokaci aka fahimci irin mummunar barnar da suka tafka.