Jami'an Tsaron Uganda Sun Tsananta Gudanar Da Matakan Tsaro A Kasar
(last modified Wed, 11 May 2016 10:22:04 GMT )
May 11, 2016 10:22 UTC
  • Jami'an Tsaron Uganda Sun Tsananta Gudanar Da Matakan Tsaro A Kasar

Jami'an tsaron Uganda sun tsananta gudanar da matakan tsaro a duk fadin kasar domin hana 'yan adawa gudanar da zanga-zangar lumana a lokacin bikin rantsar da Yoweri Musebeni a matsayin zababben shugaban kasa a gobe Alhamis.

Majiyar rundunar 'yan sandan Uganda ta sanar da cewa: Tsaurara matakan tsaro a kasar musamman birnin Kamfala yana matsayin riga kafi ne domin kalubalantar duk wata barazanar tsaro a lokacin gudanar da bikin rantsar da shugaban kasar.

Jaridar Daily Monitor ta kasar Uganda ta habarto daga babban sakataren jam'iyyar adawa ta kasar "Forum for Democratic Change" (FDC) a takaice cewa; Tun bayan karatowar lokacin bikin rantsar da shugaba Yoweri Musebeni jami'an tsaron kasar suka fara takurawa 'yan adawa ta hanyar kai farmaki kan ofisoshinsu tare da awungaba da mambobin jam'iyyar ta "FDC" da nufin dakile duk wani yunkurin nuna rashin amincewa da rashin halaccin zaben shugaba Yuweri Musebeni.