An gano tarin makamai a kan iyakakokin kasashen Mali da Aljeria
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i514-an_gano_tarin_makamai_a_kan_iyakakokin_kasashen_mali_da_aljeria
Dakarun tsaron kasar Aljeria sun gano wasu tarin makamai a kan iyakar kasar da Mali.
(last modified 2018-08-22T06:57:47+00:00 )
Feb 09, 2016 07:25 UTC
  • An gano tarin makamai a kan iyakakokin kasashen Mali da Aljeria

Dakarun tsaron kasar Aljeria sun gano wasu tarin makamai a kan iyakar kasar da Mali.

Ma'aikatar tsaron kasar Aljeria ta sanar da cewa a ci gaba da kokarin tsarkake iyakokin kasar daga 'yan ta'adda, Dakarun tsaron kasar sun gano runbun tsimin makamai a kan iyakar kasar da kasar Mali

Rahoton ya ce a cikin wannan runbun tsimi a kwai manya-manyan bindigogi kirar Kilashcop, bindigogin masu sarrafa kansu,tarun gurneti da kuma ababe masu fashewa.

A makun da ya gabata Ma'aikatar tsaron Aljerian ta sanar da kisan 'yan ta'adda guda 4 a yankin Auladul Hamidah.

Har ila yau a cikin wani rahoto da ta fitar na shekara, Ma'aikatar tsaron ta bayyana cewa a shekara ta 2015 Sojojin kasar sun hallaka 'yan ta'adda 157, bayan da suka kame kwamondojin su 10, da kuma makamai yaki 307.