EFCC Ta Tsare Mal. Shekarau Saboda Zargin Cin Kudaden Makamai
Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar (EFCC) ta kama tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan ilmi na kasar Malam Ibrahim Shekarau saboda zarginsa da hannu cikin cin wasu kudade da suka kai Naira miliyan 950 da aka ware don sayo makaman fada da kungiyar Boko Haram a kasar.
Rahotannin sun ce a jiya Alhamis ne dai tsohon ministan ilimin ya tafi ofishin hukumar ta EFCC da ke Kano don amsa gayyatar da ta yi masa domin amsa tambayoyi kan zargin ya amfana da wani bangare na na Naira miliyan 950 da aka ware don sayo makaman fada da kungiyar Boko Haram amma aka karkata akalarsu wajen yakin neman zaben tsohon shugaban Nijeriyan Goodluck Jonathan a shekarar bara.
Hukumar dai ta bukaci malam Shekarau ne da ya zo yayi mata bayani bayan da tsohon ministan harkokin wajen Nijeriya Ambassador Aminu Wali ya ambaci sunansa cikin wadanda suka amfana da wadannan kudaden. Ambasador Wali dai ya shaida wa hukumar ta EFCC a makon da ya wuce cewa shi ne ya karbo wadannan kudaden a matsayinsa na shugaban wani kwamitin na yakin neman zaben shugaba Jonathan din na jihar Kano inda ya ce ya kawo kudi inda suka raba a tsakaninsu a gidan malam Shekarau din.
Majiyoyin hukumar ta EFCC sun tabbatar da cewa suna rike da malam Shekarau din bayan sun ki ba da belinsa har sai ya cika wasu sharuddan da aka gindaya masa.