Gargadin Unicef Akan Fadace-fadace A Nahiyar Afrika
Gargardi Akan Yadda Ake Shigar Da yara cikin fadace-fadace A Nahiyar Afirka
A yau talata ne Asusun Kananan Yaran Na Majalisar Dinkin Duniyar ya fitar da bayani wanda ya kunshi gargadi akan yadda ake shigar da kanana yara cikin soja a kasashe masu yawa na Afirka.
Rahoton ya kuma ambaci cewa tattara bayanai na tsawon shekaru 20 ya tabbatar da cewa; A halin yanzu da akwai dubban kanana yara wadanda su ke cikin fadace-fadacen da ake yi.
Wani sashe na rahoton ya kuma yi nuni da kasar Yemen wacce ita ma ta ke fama da fadace-fadace da kuma yadda ake shigar da kananan yara a ciki.
Yaran da ake shigar da su a cikin yake-yaken dai shekarunsu suna kasa da 14 ne. Rahoton ya ambaci rusa makarantu da ake yi saboda fadace-fadace a matsayin wasu dalilan da su ke nesanta yaran daga yin karatu