Zanga-Zanga Akan Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i529-zanga_zanga_akan_shugaban_kasar_afirka_ta_kudu
An yi Zanga-zangar nuna kin amincewa shugaba Jacob Zuma Na Afirka ta kudu.
(last modified 2018-08-22T11:27:47+00:00 )
Feb 09, 2016 18:57 UTC
  • Zanga-Zanga Akan Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu

An yi Zanga-zangar nuna kin amincewa shugaba Jacob Zuma Na Afirka ta kudu.

Masu adawa da shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacon Zuma sun gudanar da zanga-zangar zarginsa da wasa da kasafin kudin kasar.

Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya ambato cewa; Masu Zanga-zangar da su ka kewaya titunan birnin Johannesburg sun nufi ginin kotun kundin tsarin mulkin kasar suna masu yin kira da a yi wa shugaban kasar shari'a akan wasa da kasafin kudi.

Kotun dai ta yi zama ne a yau inda ta bude bincike akan zargin da ake yi wa shugaban kasar Jacob zuwa da yin amfani da kasafin kudin kasar akan bukatunsa na kanshi.

A shekarar 2014 ne dai aka fara bankado batun na zargin shugaba Zuma da cewa shi da iyalansa sun gina wani gida daga cikin kudin kasar.

Kudaden da ake zargin Zuma da amfani da su, sun kai dalar Amurka miliyan 24.