Uganda: Ana Ci gaba Da Tsare Jagoran 'Yan hamayyar Siyasa
(last modified Wed, 18 May 2016 19:39:33 GMT )
May 18, 2016 19:39 UTC
  • Uganda: Ana Ci gaba Da Tsare Jagoran 'Yan hamayyar Siyasa

Kotun A Kasar Uganda Ta Bada Umarnin A ci gaba da tsare Kizza Besigye

Wata Kotu a kasar Uganda ta bada umarnin a ci gaba da tsare jagoran 'yan hamayyar siyasa Kizza Besigye wanda ya ke fuskantar zargin cin amanar kasa.

A yau laraba ne dai aka kai Basigye kotun a cikin matsanancin tsaro inda alkalin kotun ya karanta masa laifin da ake tuhumarsa da shi, sannan kuma ya bada umarnin da a ci gaba da tsare shi har zuwa 1 ga watan Yuni.

Cin amanar kasa da ake zargin Basigye da shi, ya kunshi tuhumarsa da shelanta kansa a matsayin shugaban kasa.

A cikin watan Febrairu ne dai aka gudanar da zaben shugaban kasar Uganda wanda aka bayyana Yoweri Musaveni a mastayin wanda ya lashe.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da aka tuhimi Besigye da cin amanar kasa, a shekarar 2005 ma ya fuskanci irin wannan tuhumar.

Lauyan da ya ke baiwa dan hamayyar siyasar kariya, Moses Byamugisha ya ce; wanda ya ke karewa din ya tsaya a gaban shari'a ba tare da wakilci na shari'a ba.

Tuni dai aka mayar da shi zuwa gidan kurkukun Luzira da ke kusa da birnin Kampala.