Mali : An Kashe Sojojin MDD Biyar A Kidal
May 19, 2016 06:05 UTC
Tawagar wanzar da zamen lafiya ta MDD a Mali ta sanar da mutuwar wasu sojojin ta 5, a wani harin kwantar bauna a arewacin Kidal.
Sanarwa ta kuma ce akwai wasu sojojin na MINUSMA uku da suka samu munanen raunuka a harin da aka kai ma ayarin motocinsu dake rakiyar motocin daukan kaya da yammacin jiya Laraba a Aguelhok.
Sojojin da suka mutu 'yan asalin kasar Chadi.
tawagar ta MINUSMA tayi allawadai da kakkausar murya da wannan harin, tare isar da ta'aziyar ta ga iyalan sojojin da suka rasun, da kuma fatan sauki ga wadanda suka raunana, tare da cewa hakan bai yi mata katsan landa ba ga aikin da take na kare al'umma da dukuyoyin a wannan kasa ta Mali.
Tags