Hallaka daya daga cikin Shugabanin kungiyoyin dake dauke da makamai a Tunusiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5386-hallaka_daya_daga_cikin_shugabanin_kungiyoyin_dake_dauke_da_makamai_a_tunusiya
Ma'aikatar tsaron Tunusiya ta sanar da hallaka wani komandan 'yan ta'adda a kasar
(last modified 2018-08-22T11:28:17+00:00 )
May 19, 2016 14:43 UTC
  • Hallaka daya daga cikin Shugabanin kungiyoyin dake dauke da makamai a Tunusiya

Ma'aikatar tsaron Tunusiya ta sanar da hallaka wani komandan 'yan ta'adda a kasar

Kafar watsa Labaran Jaridar Le figaro ta kasar Faransa ta habarta cewa Ma'aikatar tsaron Tunusiya da sanar da cewa Dakarun tsaron kasar sun nasarar Hallaka Seifeddine Jameli wanda ake kira da Abou al-Qaaqaa daya daga cikin komondodin kungiyar 'yan ta'adda Jund al-Khilafa a daren jiya Laraba, ita dai wannan kungiya ta Jund al-Khilafa nada alaka ta kut da kut da kungiyar Da'esh ko kuma ISIS a takaice, an hallaka Abou Al-Qaaqaa ne a yayin wani sumame da Sojojin kasar masu yaki da ta'addanci suka kai a tsibirin Mghilla dake yammacin kasar.

tun daga shekarar 2012 ne Dakarun tsaron na Tunusiya ke yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a tsaunukan kasar musaman tsaunin Chaambi dake jihar Kasrin wanda shine aka fi sani da tungar 'yan ta'adda a kasar.