Kungiyar Ansaruddeen Ta Dauki Alhakin Kashe Dakarun MDD A Kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5425-kungiyar_ansaruddeen_ta_dauki_alhakin_kashe_dakarun_mdd_a_kasar_mali
Kungiyar ta'addanci ta Ansaruddeen mai fada da makami a kasar Mali ta sanar da cewa ita ce ke da alhakin halaka dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a yankin arewacin kasar ta Mali.
(last modified 2018-08-22T06:58:18+00:00 )
May 20, 2016 00:08 UTC
  • Kungiyar Ansaruddeen Ta Dauki Alhakin Kashe Dakarun MDD A Kasar Mali

Kungiyar ta'addanci ta Ansaruddeen mai fada da makami a kasar Mali ta sanar da cewa ita ce ke da alhakin halaka dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a yankin arewacin kasar ta Mali.

A bayanin da kungiyar ta'addanci ta Ansaruddeen ta fitar a jiya Alhamis ta sanar da cewa: Mayakan kungiyarta ne suka kashe dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Kidel da ke arewacin kasar Mali.

A ranar Laraba da ta gabata ce majiyar rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da sanarwar cewa: Wasu gungun 'yan bindiga sun kai farmaki kan dakarunta da suke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin da Kidel, inda suka kashe sojojin biyar tare da jikkata wasu uku na daban.

Wasu rahotonni sun bayyana cewa; Dukkanin sojojin biyar da suka kwanta dama sojojin kasar Chadi ne.