Kame Jagoran 'yan hamayyar Kasar Uganda.
Jagoran hamayyar siyasar kasar Uganda, Kizza Besigye yana fuskantar shari'a bisa zargin cin amanar kasa.
Kotun da ta fara yi masa shari'a a shekaran jiya laraba ta bada umarnin da a ci gaba da tsare shi, har zuwa watan Yuni.
Shi dai Besigye ya bayyana kansa a matsayin halartaccen shugaban kasa, adaidai lokacin da aka rantsar da shugaba Uweri Musaveni.
'Yan sanda sun zargi Besigye din da kokari haddasa tashin hankali a cikin babban birnin kasar Kampala.
Zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 18 ga watan febrairu ya haddasa jayayya a tsakanin magoya bayan shugaban kasar da kuma 'yan hamayya.
Jagoran hamayyar siyasar ta Uganda ya bayyana zaben da aka yi da cewa yaudara ce. Magoya bayansa kuma sun rika gudanar da zanga-zanga da kuma gangami domin nuna kin yardarsu da sakamakon zaben, suna masu yin kira da a sake kidayar kuri'u.
Wannan, ba shi ne karon farko ba da Yewuri Musaveni ya fuskanci kalubale a yayin zabe. A karon farko ya dare kan karagar mulkin kasar ne da a 1986. Ya kuma tafiyar da mulkin kasar ne a karkashin jam'iyya daya tilo tare kuma da amfani da karfi.
Sai dai bayan matsin lamba daga cikin gida da kuma waje, Mosaveni ya amince da yin sabon kundin tsarin mulki a 2005 wanda kuma al'ummar kasar su ka kada kuri'ar raba gardama akansa.
Bayan amincewa da sabon kundin tsarin mulkin, ya fito da wata dabara ta yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima a majalisar kasar, da ta kai ga sauya duk wata ayar doka da za ta yi wa mulkinsa iyaka.
A gefe daya matakan da shugaba Mosaveni ya ke dauka na kara riko da madafan iko, ya fusata 'yan hamayyar siyasar kasar. Haka nan kuma koma bayan tattalin arzikin da kasar ta rika fuskanta ya jefa makomar kasar cikin damuwa.
'Yan hamayyar siyasar kasar ta Uganda, suna kallon shugaba Mosaveni a matsayin mai kare manufofin kasashen turai, gabanin kare manufofin kasar.
Masharhanta suna bayyana damuwarsu akan abinda ya ke faruwa a cikin kasar ta Uganda, sai kuma wasu suna ganin cewa ba a kai ga gacin da za a iya tunanin kasar Uganda ba tare da Mosaveni ba.