Chadi : Jam'iyya Mai Mulki Ta Tsaida Idris Deby Takarar Shugaban Kasa
Feb 10, 2016 11:55 UTC
A ranar 10 ga watan Afrilu mai zuwa al'umma a kasar Chadi ke kada kuri'a a zaben shugaban kasa.
Jam'iyyar MPS mai mulki a kasar Chadi ta tsaida shugaba mai ci Idriss Deby Itmo a matsayin dan takaran ta a zaben shugaban kasar mai zuwa.
A ranar 10 ga watan Afrilu mai zuwa al'umma a wannan kasa ke kada kuri'a a zaben shugaban kasa.
Idriss Deby wanda ya kama mulki bayan hambarar da gwamnatin Hissène Habré a shekara 1990, ya zama shugaban kasar Chadi har sau hudu a jere kuma a koda yaushe yakan lashe zaben ne da gagarimin rinjaye.
Tags