Chadi : Jam'iyya Mai Mulki Ta Tsaida Idris Deby Takarar Shugaban Kasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i556-chadi_jam'iyya_mai_mulki_ta_tsaida_idris_deby_takarar_shugaban_kasa
A ranar 10 ga watan Afrilu mai zuwa al'umma a kasar Chadi ke kada kuri'a a zaben shugaban kasa.
(last modified 2018-08-22T06:57:47+00:00 )
Feb 10, 2016 08:25 UTC
  • shugaban Chadi Idriss deby
    shugaban Chadi Idriss deby

A ranar 10 ga watan Afrilu mai zuwa al'umma a kasar Chadi ke kada kuri'a a zaben shugaban kasa.

Jam'iyyar MPS mai mulki a kasar Chadi ta tsaida shugaba mai ci Idriss Deby Itmo a matsayin dan takaran ta a zaben shugaban kasar mai zuwa.

A ranar 10 ga watan Afrilu mai zuwa al'umma a wannan kasa ke kada kuri'a a zaben shugaban kasa.

Idriss Deby wanda ya kama mulki bayan hambarar da gwamnatin Hissène Habré a shekara 1990, ya zama shugaban kasar Chadi har sau hudu a jere kuma a koda yaushe yakan lashe zaben ne da gagarimin rinjaye.