'Yan Adawa Sunyi Zanga-Zanga A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5581-'yan_adawa_sunyi_zanga_zanga_a_mali
Dubun dubatar jama'a ne a Mali suka gudanar da wata zanga-zangar lumana yau Asabar bisa ga kiran 'yan adawa na kasar akan abunda suka kira rashin iya tafiyar da mulki na gwamnatin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:19+00:00 )
May 21, 2016 11:30 UTC
  • 'Yan Adawa Sunyi Zanga-Zanga A Mali

Dubun dubatar jama'a ne a Mali suka gudanar da wata zanga-zangar lumana yau Asabar bisa ga kiran 'yan adawa na kasar akan abunda suka kira rashin iya tafiyar da mulki na gwamnatin kasar.

Masu zanga-zanga dai na dai na raira taken allawadai da salon mulki kasar, da matsalar tsaro da yinwa da al'ummar kasar ke fama da ita, tare da cewa shugaban kasar IBK bai cika al'kawarinsa ba.

Jagoran 'yan adawa na kasar Soumaila Cisse na jam'iyyar URD wanda shi ma ya halarci zanga-zangar ya shaidawa masu aiko da rahatanni cewa kasar na cikin halin damuwa saboda rashin iya tafiyar da mulki.

Haka zalika a cikin maharta zanga-zanga hadda magoya bayan tsohon shugaban kasar Amadou Toumani Touré, wanda suke kira gare sa daya dawo kasar.

Kasar Mali dai na fama da matsalar rashin tsaro musamen a arewacin ta wanda ke zamen babban kalubale gare ta dama kasashen makoftan ta.

hakan ne ma yasa kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ke nazarin kafa wata rindinar hadin gwiwa sojojin kasashen yankin domin tabbatar da tsaro a arewacin Mali wanda ke zaman wata cibiyar hada duk wata manakisa ta 'kungoyoyi masu tsasauran ra'ayi addini kamar yadda shugaban kasar Nijar ya shaida a wata ganawa da takwaran sa Alhassan Watara na cote d'Ivoire.