Gwamnatin Kasar Canada Zata Tallafawa Kasar Tunisia Kan Harkokin Tsaro
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5596-gwamnatin_kasar_canada_zata_tallafawa_kasar_tunisia_kan_harkokin_tsaro
Gwamnatin kasar Canada zata tallafawa kasashen arewacin Afrika ukku a fagen kyautata harkokin tsaro a yankin.
(last modified 2018-08-22T11:28:19+00:00 )
May 22, 2016 04:14 UTC
  • Gwamnatin Kasar Canada Zata Tallafawa Kasar Tunisia Kan Harkokin Tsaro

Gwamnatin kasar Canada zata tallafawa kasashen arewacin Afrika ukku a fagen kyautata harkokin tsaro a yankin.

Gwamnatin kasar Canada zata tallafawa kasashen arewacin Afrika ukku a fagen kyautata harkokin tsaro a yankin.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Canada Stephane Dion wanda yake ziyarar aiki a birnin Tunis na kasar Tunisia a jiya Asabar yana fadar haka, ya kuma kara da cewa a cikin shekaru ukku masu zuwa gwamnatinsa zata tallafawa wadan nan kasashen a fagen yaki da ayyukan ta'addanci.

Stephane Dion ya kara da cewa kasarsa zata kashe dalar Amurka milion 4 a kasar Tunisia don kyautata harkokin tsaro a kasar, wanda kuma zai kyauatta tattalin arzikin kasar. Ministan ya kuma yi kira ga kasashen yamma da su tallafawa gwamnatin kasar Tunisia a kokarin da take yi na yakar yan ta'adda.

A shekara ta 2015 da ta gabata ce yan ta'adda suka kai wani mummunan hari kan masu yawan shakatawa a kasar ta Tunisia wanda ya kai ga mutuwar mutane 74 mafi yawansu sun fito ne daga kasashen Yamma. Ana saran kasashen Amurka, Britania da kuma Faransa zasu bada nasu gudumawar ga kasar Tunisia kan wannan lamarin.