Kungiyar Ta'addanci Ta Da'ish Ta Kashe Tsohon Ministan Ayyuka Na Kasar Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5623-kungiyar_ta'addanci_ta_da'ish_ta_kashe_tsohon_ministan_ayyuka_na_kasar_libiya
Dauki ba dadi tsakanin rundunar sojin gwamnatin hadin kan kasa a Libiya da mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish ya lashe ran tsohon ministan ayyukan kasar a yammacin kasar Libiya.
(last modified 2018-08-22T06:58:19+00:00 )
May 22, 2016 13:05 UTC
  • Kungiyar Ta'addanci Ta Da'ish Ta Kashe Tsohon Ministan Ayyuka Na Kasar Libiya

Dauki ba dadi tsakanin rundunar sojin gwamnatin hadin kan kasa a Libiya da mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish ya lashe ran tsohon ministan ayyukan kasar a yammacin kasar Libiya.

Kafar watsa labaran Libiya ta "LANA" a yau Lahadi ta bada labarin cewa: Gumurzu tsakanin rundunar sojin gwamnatin hadin kan kasa a Libiya da mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish ya yi sanadiyyar mutuwar Muhammad Sawa'lim tsohon ministan ayyuka a gwamnatin fira minista Ali Zaidan a yankin Abu-Qarin da ke nisann kilomita 100 da garin Sirt a yammacin kasar.

Tsohon ministan Muhammad Sawa'lim shi ke jagorantar rundunar sojin sabuwar gwamnatin hadin kan kasa a Libiya a yakin da ta daura da kungiyar ta'addanci ta Da'ish a yankin yammacin kasar.

A gefe guda kuma jirgin saman yakin rundunar sojin ta Libiya ya samu nasarar yin luguden wuta kan tawagar motocin mayakan kungiyar ta Da'ish da suke gumurzu da sojojin gwamnati inda ya tarwatsa motoci da dama tare da halakar 'yan ta'addan da suke cikin motocin.