Karfafa matakan tsaro na yaki da ta'addanci a Aljeriya
Kasar Aljeriya ta karfafa matakan tsaron a yankunan da ake tono iskar gaz
Bayan harin da 'yan ta'adda suka kai kan kamfanin isgar gaz na Jihar Ainul Salah dake kudancin kasar Aljeriya, A yau Assabar Dakarun tsaron kasar sun sanar da karfafa matsalar tsaro a gurin domin tunkarar duk wani ta'addanci.
Jihar Ainul Salah na daga cikin manyan buranan kasuwancin kasar , inda a can ne babban kamfanin iskar Gaz din kasar Sounatrac da na kasashen wajen suke.
Wannan dai ba shi ba ne karo na faro da 'yan ta'addar ke kaiwa kamfanin iskar Gaz din na Aljeriya hari tun bayan mumunan harin da aka kaiwa Kamfanin Iskar Gaz din kasar na jihar En Eminas dake kudancin kasar a shekarar 2013.
A gafe guda Dakarun tsaron Aljeriyan na ci gaban da samun nasara a yakin da suke yi da 'yan ta'adda a kan iyakar kasar da Libiya.