An gano runbun-tsumin makamai a kan iyakar kasashen Aljeriya da Mali
Ma'aikatar tsaron Aljeriya ta sanar da gano wani runbuntsimin makamai a kan iyakar kasar ta da kasar Mali.
A cikin wata Sanarwa da ta fitar yau Litinin Ma'aitar tsaron Aljeriyan ta sanar da nau'in makaman da Dakarun tsaron kasar suka gano wadanda suka hada da bindigogi kirar Kalashcop, gurneti da kuma Nakiyoyi da dama gami da wasu nau'in bindigogi kimanin dubu guda.
Kafin hakan, Dakarun tsaron kasar sun gano maboyar 'yan ta'adda da makamai da dama tare da rusa su a cikin kasar.
A bangare guda, Dakarun tsaron Aljeriyan sun hallaka wasu Mutane da ake zarkin 'yan ta'adda guda 12 a kudu maso gabashin kasar.
Tun daga ranar 17 ga wannan wata na Mai ne Dakarun tsaron kasar suka fara farautar 'yan ta'adda da nufin yaki da ta'addanci.