Hukuncin Daurin Rai Da Rai Kan Tsohon Shugaban Kasar Chadi Husain Habre
(last modified Wed, 01 Jun 2016 05:52:05 GMT )
Jun 01, 2016 05:52 UTC
  • Hukuncin Daurin Rai Da Rai Kan Tsohon Shugaban Kasar Chadi Husain Habre

Husasin Habre zai gudanar da sauran rayuwarsa a cikin kurkuku idan kotu ta sama ta tabbatar da hukuncin da aka yanke masa

A cikin makon da muke ciki ne wata kotu a kasar Senegal ta yanke hukuncin daurin rai da rai kan tsohon shugaban kasar Chadi Husain Habre, wanda ya kawo karshen gwagwarmayan da ya yi take da hukumomi daban daban kan shari'arsa na tsawon shekaru 17.

Husain Habre dan shekara 73 a duniya ya musanta dukkan zargin da ake masa kan cin zarafin bil'adama a cikin shekaru 8 da ya yi yana shugabancin kasar ta Chadi.

Wani komitin bincike wanda gwamnatin Idris Debi shugaban kasar Chadian a yanzu ta kafa don binciken irin laifuffukan cin zarafin bil'adama wanda jami'an tsaron Chadi karkashin shugabancin Habre suka aikata ya nuna cewa, an kasha mutane 40,000 kan akidarsu ta siyasa a kasar, sannan wasu 200,000 an azabtar da su a tsakanin shekara 1982-1990 da Habre ya shugabanci kasar.

Tun bayan an masa juyin mulki ne ya arce zuwa kasar Senegal inda ya sami mafakar siyasa ya kuma yi aure harma ya haifi yayansa guda hudu a can.

Husain Habre dai ya tashi ne a cikin kabilar Toubou makiyaya a arewacin kasar ya kuma kamala karatunsa na Jami'a a ne kasar faransa.

A shekara ta 1974 sunan Husain Habre ya fara fice a duniya a lokacinda ya jagoranci kungiyarsa ta yan tawaye suka sace Turawa guda ukkua sannan ya nema kudin farsarsu na saifa miliyin 10.

Bayan haka ne gwamnatocin kasar Amurka ta Faransa suka tallafawa Husain Habre ya yi wa Gokuni Odai juyin mulki ya kuma sami nasarar kori sojojin kasar Libya daga kasar ta chadi wadanda suka shiga kasar kan rigimar kan iyaka na yankin Aozou da kasar a shekara ta 1982 -1983.

A lokacin mulkinsa ya fuskanci ya tawaye daga kabilun kasar daban daban, wadanda suke zarginsa da azabtar da su. Wannan halin ya ci gaba har zuwa lokacinda kungiyar yan tawaye ta Idris Debi suka kore shi daga kasar.

Bayan da wadanda abin ya shafa suka matsa kan a gurfanar da Husain Habre a gaban kuliya gwamnatin kasar Senegal da farko tace bata da hurumin gurfanar da wani wanda ya aikata laifi a kasashen waje a cikin kasar.

Bayan haka ne suka koma kasar Belguim, bayan shekaru hudu sai wata kotu a kasar ta bada sammacin kama shi a shekara 2005, don a gurfanar da shi a kasar. A nan ne gwamnatin kasar Senegal ta yi masa daurin talala a cikin gidansa a birnin Daka. Daga baya shugaban kasar Senegal na lokacin Abdalla Wad ya bayyana cewa kasarsa bata da kudaden gurfanar da shi a gaban kuliya. Sannan ya ki amincewa a mika shi ga kasar Belguim . A nan ne kungiyar tarayyar Africa ta bukaci gwamnatin kasar Senegal ta kafa kotu wacce zata hukuntaci. Shugaban ya amince da hakan a shekara 2008, inda ya bukaci a sauya dokokin kasar Senegal ya yadda zasu bashi damar yiwa Husain Habre hukunci a cikin kasara.

Ana cikin haka ne sai gwamnatin kasar Senegal ta bada sanarwan cewa zata mikashi ga gwamnatin kasar Chadi don a gurfanar da shi a kasarsa, amma majalisar dinkin duniya ta shiga tsakani ta kuma hana a maida shi kasarsa don ganin cewa tuni an rika an yanke masa hukuncin kisa , don haka an an mika shi zata kasha shi ne kawai. Don haka aka dakatar da wanna shirin.

Sai kuma a shekara ta 2012 kotun kasa da kasa ta ICC ta bukaci gwamnatin kasar Senegal ta gurfanar da shi a gaban kotu a kasar ko kuma da mika shi ga kasar Belguim. Daga karshe tarayyar Afrika ta cimma yerjejeniya da gwamnatin Senegal ta kafa kotu a cikin kasar ta kuma gurfanar da shi a cikin kasar.

Kafin a gurfanar da shi a gaban kotu a cikin yan watanni da suka gabata Husain Habre yana rayuwa ne tare da matarsa da kuma yayansa hudu a cikin birnin Daka, inda ake iya ganinsa yana fita zuwa masallacin jumma'a a ko wani mako.

A halin yanzu dai tsohon shugaban kasar na chadi yana da damar daukaka kara kan hukuncin daurin rai da rai da aka yanke masa, idan kotun daukaka karan ta tabbatar da hukuncin, wannan ya nuna cewa Husasin Habre zai gudanar da sauran rayuwarsa a cikin kurkuku.