An Kai Hari Kan Sansanin Sojojin Majalisar Dinkin Duniya A Mali
Jun 01, 2016 05:55 UTC
Kamfanin dillancin labaran AFP daga birnin Bamako na kasar Mali ya habarta cewa, wasu masu dauke da makamai sun kaddamar da wani farmaki a kan wani sansanin dakarun MDD a yankin Gao, wanda ya yi sanadiyyar mutane 4.
A cikin wani bayani da rundunar ta MDD ta fitar ta bayayna cewa, daya daga cikin wadanda suka rasa rayukansu sojan kasar China da ke a karkashin rundunar, yayin da sauran uku kuma fararen hula.
Bayanin ya ce wannan aikin ta'addanci ba zai taba hana MDD ci gaba da gudanar da aikin wanzan da zaman lafiya akasar Mali ba.
Tags