An Halaka Yan Ta'adda 8 A Arewacin Kasar Algeria A Yau Laraba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6109-an_halaka_yan_ta'adda_8_a_arewacin_kasar_algeria_a_yau_laraba
Majiyar sojojin kasar Algeria ta bada sanarwan halaka yan ta'adda guda 8
(last modified 2018-08-22T06:58:22+00:00 )
Jun 01, 2016 12:57 UTC
  • An Halaka Yan Ta'adda 8 A Arewacin Kasar Algeria A Yau Laraba

Majiyar sojojin kasar Algeria ta bada sanarwan halaka yan ta'adda guda 8

Majiyar sojojin kasar Algeria ta bada sanarwan halaka yan ta'adda guda 8 a wani sumamen da sojojin kasar suka kai zuwa wani wuria a lardin Setf daga arewacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar sojojin tana bayyana haka a yau Laraba ta kuma kara da cewa a jiya da daren ne sojojin suka kai sumamen a garin Kal'e zar'aa mai tazarar kilomita 280 daga babban birnin kasar, kuma cikin lardin Setif inda suka rusta da yan ta'addan suka kashe 8 daga cikinsu suka kuma gano makamai da dama a mabuyarsu.

A cikin kwanaki 10 da suka gabata majaiyar sojojin na Algeria ta bayyana cewa ta rutsa da yan ta'adda da dama a yankin gabacin kasar inda nan ma suka kashe yan ta'adda 6 suka kuma karbe makamai da dama daga hannunsu.

Tun farkon wannan shekara ne gwamnatin kasar Algeria ta kuduri anniyar ganin bayan yan ta'adda a cikin kasar.