Ban Ki Moon Ya Yi Allawadai Da Harin Ta'addanci A Kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6151-ban_ki_moon_ya_yi_allawadai_da_harin_ta'addanci_a_kasar_mali
Babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya yi Allawadai da kakkausar murya dangane da harin da aka kai kan sansanin dakarun majalisar dinkin duniya a kasar Mali.
(last modified 2018-08-22T06:58:22+00:00 )
Jun 02, 2016 06:28 UTC
  • Ban Ki Moon Ya Yi Allawadai Da Harin Ta'addanci A Kasar Mali

Babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya yi Allawadai da kakkausar murya dangane da harin da aka kai kan sansanin dakarun majalisar dinkin duniya a kasar Mali.

Kamfanin dillancin labaran Afp ya habarta cewa, Ban Ki Moon ya yi Allawadai da harin na jiya wanda wasu amsu dauke da makamai suka kai kan sansanin dakarun majalisar dinkin duniya a yankin Gao da ke arewacin kasar, inda mutane 4 suka rasa rayukansu, da suka hada da wani sojan kasar China da ke aiki a cikin wannan runduna.

A cikin kasa da wata guda, dakarun majalisar dinkin duniya 12 suka rasa rayukansu a kasar Mali, yayin da wasu da dama suka samu raunuka, sakamakon hare-haren da masu dauke da makamai da ake da alaka da kungiyoyi masu da'awar jihadi ke kaiwa a kansu.