An buda taron kungiyar CEDEAO a kasar Senegal
(last modified Sat, 04 Jun 2016 19:00:41 GMT )
Jun 04, 2016 19:00 UTC
  • An buda taron  kungiyar CEDEAO a kasar Senegal

An bude Taro ECOWAS karo na 49 a birnin Dakar na kasar Senegal

A safiyar yau Assabar ne kungiyar bunkasa tattalin Arzikin kasashen yammacin Afirka Ecowas ta fara gudanar da taronta karo na 49 a birnin Dakar na kasar Senegal, taron ya samu halartar wasu daga cikin shugabanin kasashen kungiyar mai manbobi 15.

Ganin yadda kasashen dake cikin wannan kungiya suka fuskanci matsalar tsaro a cikin 'yan watanin nan, rahotanni na cewa taron zai fi maida hankali ne kan harakokin tsaro.

Har ila yau ana sa ran taron zai tattauna kan samar da wani yanki na kasuwanci tsakanin kungiyar kasashen turai da kasashen Afirka da zai dauki tsahon lokaci na shekaru 25 masu zuwa.

Kungiyar kasashen Turai ta ce a ranar 25 na watan Oktoba mai zuwa ne ake sa ran za sanya hanu kan cimma yarjejjeniyar kasuwancin tsakanin kungiyar da kungiyar kasashen Afirkan.

A halin yanzu, Shugaban kasar Senegal Macky Sall shi ke jagorantar kungiyar bunkasa tattalin Arzikin yammacin Afirkan ECOWAS ko kuma CEDEAO.