Senegal ta jaddada Ci gaba da Fada da ayyukan ta'addanci a Afirka.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6259-senegal_ta_jaddada_ci_gaba_da_fada_da_ayyukan_ta'addanci_a_afirka.
Shugaban Senegal Ya jaddada wajabcin ci gaba da fada da masu wuce gona da iri a cikin nahiyar.
(last modified 2018-08-22T06:58:23+00:00 )
Jun 05, 2016 03:03 UTC
  • Senegal ta jaddada  Ci gaba da Fada da ayyukan ta'addanci a Afirka.

Shugaban Senegal Ya jaddada wajabcin ci gaba da fada da masu wuce gona da iri a cikin nahiyar.

Shugaba Macky Salla wanda ya ke gabatar da jawabin bude taron shekara-shekara na kungiyar kasashen Afrika ta yamma ya ce; Hare-haren da ake kai wa a Najeriya da Nijar da Mali yana nuni da cewa da akwai barazanar mai girma da yankin yammacin Afirka ya ke fuskanta daga 'yan ta'adda.

Shugaban na Senegal da kasarsa ta ke karbar bakuncin taron kasashen yammacin Afirka ya ci gaba da cewa wajibi ne a yi aiki tare a tsakanin kasashen domin fada da ta'addancin.

HAr ila yau, shugaban na kasar Sengala ya yi ishara da mummunan harin da aka kai a Dosso a jiya asabar sannan kuma ya isar da sakon ta'aziyyarsa ga shugaba Muhammadu Issoufu.

Ita dai kungiyar Cedeao, an kafa ta ne tun a 1975, kuma tanada mambobi 15 da su ka kunshi; Benin da Bornika Faso da Cote De Voire da Ghana da Gambia da Cape Verd. Sai kuma kasashen Mali da Liberia da Gunea Bissau da Najeriya da Nijar da Saliyo da Senegal da Togo.