Afirka Ta Kudu : Babu Damuwa Dangane Da Barazanar Kai Hari
Jun 06, 2016 10:42 UTC
Gwamnatin Afirka ta kudu ta fitar da sanarwar cewa babu wata damuwa dangane da barazanar kai hari a kasar.
Wannan dai ya biyo bayan gargadin da offishin jakadancin Amurka ya yi dangane da yiwuwar kai hare-haren ta'adanci a wannan kasa.
Ministan kula da harkokin tsaro na Afrika ta kudu ya ce zasu dauki batun da mahimmanci, aman dai kayo yanzu babu wata damuwa dangane da wannan barazana.
Tags