'Yan Boko Haram Sun Sake Kwace Garin Bosso Na Jamhuriyar Nijar
Rahotanni daga kasar Nijar suna nuni da cewa 'yan kungiyar nan ta Boko Haram sun sake kwace garin Bosso da ke kan iyakan kasar da Nijeriya a yau din nan Litinin bayan da sojojin kasar suka kwace shi daga hannunsu a shekaran jiya.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto wata majiyar sojin ta Nijar tana bayyana cewar bayan wani gumurzu mai tsanani da ya gudana tsakanin sojoji da 'yan Boko Haram din a daren jiya, maharan Boko haram din sun sake kwace garin na Bosso.
A ranar Juma'ar da ta gabata ce dai 'yan Boko Haram din suka fara kwace garin na Bosso da ke jihar Diffa na Jamhuriyar ta Nijar a wani harin da suka kai inda suka kashe wasu sojojin Nijar su 30 da wasu na Nijeriya su 2, sai dai kuma sojojin na Nijar da suke samun daukin na Nijariya sun sake kwace garin a ranar Asabar din da ta gabata.; sai dai kuma a daren jiya Lahadin 'yan Boko Haram din sun sake kwace garin kamar yadda magajin garin Mamadou Bako ya tabbatar.
Harin na ranar Juma'a dai shi ne irin mafi muni da 'yan kungiyar ta ta'addanci suka kai Nijar tun wani hari da suka kai garin Karamga a watan Aprilun 2015 a kasar da yayi sanadiyyar mutanen alal akalla mutane 74 da raunata wasu da dama.