Gwamnatin Kasar Uganta Ta Bayyana Sunayen Sabbin Majalisar Mistocin Kasar
(last modified Tue, 07 Jun 2016 06:55:53 GMT )
Jun 07, 2016 06:55 UTC
  • Gwamnatin Kasar Uganta Ta Bayyana Sunayen Sabbin Majalisar Mistocin Kasar

Shugaban kasar Uganda ya bada sanarwan kafa sabon majalisar ministocin kasar

Shugaban kasar Uganda ya bada sanarwan kafa sabuwar majalisar ministocin kasar. Kamfanin dillancin labaran Chinhuwa na kasar China ya nakalto shugaban Yoweri Museveni yana bada sanarwan kafa majalisar ministocin sabuwar gwamnatinsa a jiya Litinin. Inda ya kara da cewa ya nada ministoci 31 da kuma kananan ministoci masu bada shawara 49.

Bayanan da suka fito daga fadar shugaban kasar sun kara da cewa Edward Ssekandi shi ne mataimakin shugaban kasa, Ruhakana Rugunda kuma shi ne Priminister, Matia Kasaija a matsayin ministan kudi, Sam Kutesa kuma ministan harkokin waje, sai kuma Irene Muloni a matsayin ministan makamashi da kuma Kahinda Otafiire a matsayin ministan sharia.

Bayanan sun kara da cewa shugaban ya kirkiro sabbin ma'aikatu wadanda suka hada da ma'aikatar ilimi da fasaha da kuma ta tsoffin sojoji. A ranar 12-Mayu da muke ciki ne shugaba Yuweri Museveni zai yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Uganda karo na biyar.