Za A Kara Yawan Dakarun Majalisar Dinkin Duniya A Mali
Babban kwamandan dakarun majalisar dinkin duniya akasar Mali ya bayyana cewa za a kara yawan dakarun domin gudanar da ayyukan wanzar da sulhu a kasar.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, Babban kwamandan dakarun majalisar dinkin duniya a kasar Mali Mahamat Saleh Annadif ya bayayna cewa, bisa la'akari da irin barazanar da tsaro da ke ta karuwa a kasar Mali, Majalisar dinkin duniya ta amince za ta kara yawan dakarunta a kasar.
A cikin 'yan kwanakin nan dai masu da'awara jihadi suna tsananta hare-harensua yankunan arewacin kasar ta Mali, inda a baya-bayan nan suka kaddamar da hari kan sansanin dakarun na Majalisar dinkin duniya da ke yankin Gao, inda suka kashe mutane 4.