Dambaruwar Siyasa A Kasar Uganda
(last modified Sat, 11 Jun 2016 18:51:34 GMT )
Jun 11, 2016 18:51 UTC
  • Dambaruwar Siyasa A Kasar Uganda

An kame Jami'an Gwamnati 30 A Kasar Uganda Bisa Zargin Yunkurin Kifar da gwamnati.

Kafar watsa labaru ta Africa Times ya ambato kakakin sojan kasar ta Uganda janar Pady Ankonda yana cewa; Daga cikin wadanda aka kama din da akwai wani dan majalisa da kuma sojoji."

Bugu da kari janar Ankondan ya ce jami'an tsaron kasar, wato 'yan sanda suna ci gaba da gudanar da bincike tare da mutanen."

A gefe daya jaridar Monitor ta nakalto wani babban jami'in tsaron kasar Hassan Kato yana cewa; Wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a cibiyar sojan kasar da ke garin Gulo a arewacin kasar.

Kawo ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan wadanda su ka kai harin ko kuma manufarsa.

Tun bayan zaben shugaban kasar da aka yi a kasar ta Uganda, rikicin siyasa ya kunno kai saboda kin amincewar jam'iyyun hamayya da sakamakonsa da ya bai wa Yewure Musaveni rinjaye.