An yi wa Gwamnatin Aljeriya garan bawul
Shugaban Kasar Aljeriya ya nada sabbin ministocin makamashi da kudi a kasar
A jiya Assbar Shugaban kasar Aljeriya Abdul-Azizi Butalfika ya nada Nurudin Boutarifa shugaban kamfanin makamashin Sounel-Gaz na kasar a matsayin Sabon Ministan Makamashi wanda ya maye gurbin Salih Khabri, sannan kuma ya nada Haji baba Amy mataimakin ministan kasafin kudin a matsayin sabon ministan kudi wanda ya maye gurbin Abdurrahaman bn Khalifa.
Wannan sauyin dai na a matsayin kokarin da Gwamnatin Aljerian ke yi na tunkarar faduwar farashin Man fetur da isgar Gaz a Duniya, domin mafi yawan kudaden dake shigowa kasar ta hanyan Man fetur da Isgar Gaz ne.
Ya zuwa yanzu kasar ta Aljeriya ta dauki matakai da dama domin cike gibin kudaden da suke shiga cikin aljihun gwamnati inda aka kara kudaden wutar Lantarki da sauransu, lamarin da ya janyo cece kuce a tsakanin Al'ummar kasar.